Tare da yawan mutane miliyan 150 dake amfani da tsarin sadarwa na duniya na wayar salula (GSM) a cikin kasar, gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Talata cewa, tana fatan janyo karin masu samar da ayyukan sadarwa domin kara karfafa karfi a cikin tsarin wayar da ba ta girke ba wato cewa da wayar salula a cikin kasar.
Ministan sadarwar kasar, Adebayo Shittu, ya bayyana a birnin Abuja cewa, ganin yadda yawan dake karuwa na kamfanonin sadarwa da suka shiga a bangaren sadarwa, dole ne za a iya samun gogayya da kuma ingancin wannan sha'ani tsakanin masu samar da wannan aiki.
Gogayya za ta kai ga inganci, kana kuma za ta kai ga farashin kira ya yi sassauci, in ji ministan, tare da kara bayyana cewa, abun da Najeriya take bukata a halin yanzu, shi ne tsari mai inganci.
A cewar mista Shittu, Najeriya tana fatan janyo karin masu samar da ayyukan sadarwa a cikin kasar domin ba da kwarin gwiwa ga masu zuba jari shiga yankunan karkara, da kuma tabbatar da samar da tsarin sadarwa na duniya ga mazauna karkara. (Maman Ada)