in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta samu gagarumin sauyi a fannin fasahar sadarwa
2016-09-06 10:39:06 cri

Mahukunta a Najeriya sun sanar a jiya Litinin cewa, kasar ta samu gagarumin ci gaba a fannin fasahar sadarwa (ICT), inda aka samu ci gaban layukan sadarwa daga adadin kasa da 500,000 a shekarun da suka gabata zuwa miliyan 157 a halin yanzu.

Mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta kasar NCC Umar Danbatta, ya fada a birnin Legas cewa, a halin yanzu, an samu karuwar hanyoyin sadarwa a kasar daga kashi 100 zuwa kashi 107, sannan an samu karuwar kashi 97 na kafofin sadarwa ta internet a kasar.

Da yake gabatar da jawabi a taron masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa na kasa da kasa na shekarar 2016, Danbatta ya ce, sama da dala biliyan 35 aka zuba jari na kasashen waje a fannin kamfanonin sadarwa a kasar.

Ya kara da cewa, an samu jarin cikin gida na biliyoyin daloli cikin shekaru 15 a kasar.

A cewarsa, a halin yanzu kashi 14 cikin 100 ake da shi na karfin yanayin shiga kafofin sadarwa na internet a kasar, maimakon kashi 100 da ake da bukatarsa.

Danbatta ya ce ana fata nan da shekara ta 2018 za'a samu kashi 30 cikin 100 na karfin yanayin sadarwa ta internet a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China