A wata sanarwar da ma'aikatar kula da kamfanoni da fasahar sadarwa ta kasar Sin (MIIT) ta fitar, ta ce, za'a sanar da sunayen kamfanoni ko daidaikun jama'a da aka samu da laifin yin damfara ta hanyar kafofin sadarwa.
MIIT ta bukaci kamfanoni da su dakile duk wani yunkuri na masu yin damfara ta kafofin sadarwa da zarar 'yan damfarar suka bukaci aikata hakan.
Zuwa karshen shekarar nan ta 2016, kamfanonin sadarwa za su tabbatar da kammala yin rijistar masu ta'ammali da su na hakika.
Wannan mataki ya biyo bayan samun kiraye kiraye ne na neman daukar matakai kan masu aikata zamba da yin damfara ta hanyoyin sadarwa na zamani a fadin kasar, lamarin da ke haddasa yawaitar hasarar dukiyoyin jama'a.
A shekarar 2015, kasar Sin ta yi nasarar gano masu aikata damfara ta hanyar kafofin sadarwa sama da dubu 590, wadanda suka damfari kudi da ya kai RMB yuan biliyan 22.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.3. (Ahamd Fagam)