in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da manufofin raya sha'anin sadarwa
2016-07-27 21:25:24 cri
A yau Laraba ne, Sin ta gabatar da manufofin raya sha'anin sadarwa, kasar Sin za ta gudanar da wadannan manufofi ne cikin shekaru 10 masu zuwa. Kasar Sin tana shirin mallakar dukkan manyan fasahohin da ake bukata wajen raya aikin sadarwa ya zuwa shekara ta 2025.

Hakazalika, Sin tana shirin bullo da manyan kafofin sadarwa na kasa da kasa hudu wadanda za su hade yankin tekun Pasifik, tsakiya da gabashin Turai, yammaci da arewacin nahiyar Afirka, kudu maso gabashin nahiyar Asiya, tsakiyar nahiyar Asiya, da sauran kasashe da yankuna, tare da samun wasu manyan kamfanonin sadarwa nata da ke gudanar da ayyukansu a kasashen duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China