in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar jarin waje na kara bunkasa fasahohin sadarwa a Afrika
2015-06-11 10:33:13 cri

Karuwar jarin kai tsaye daga waje zuwa Afrika na rura ci gaban fasahohin sadarwa na zamani ICT a nahiyar, in ji kwararru a wannan fanni a ranar Laraba.

Ali Bofulo, darektan harkoki a cibiyar kamfanin Iway Africa Service, ya bayyana a birnin Nairobi cewa, ci gaban ababen more rayuwa, gidajen jama'a, sufuri da masana'antu, na kara bukatun ayyukan bangaren fasahohin zamani.

Ayyukan ICT sun kasance wani tushen ci gaba ga sabbin jari zuwa nahiyar Afrika, in ji mista Bofulo a yayin wani taron manema labarai kan sabbin kayayyakin masu jan hankali da fasahohin da ke nasaba da gine ginen ICT na kamfanoni.

Afrika ta zama tamkar wata mai taka rawa da ke tasowa ta fuskar kirkire kirkire na samun fita a bangaren ICT, in ji mista Bofulo.

Rashin karfin gine gine ya sanya kirkire kirkire da dama da aka yi ana amfani da su a sauran kasashen duniya, in ji masanin tare da nuna cewa, ICT na iyar taimakawa Afrika kamo jinkirinta da sauran duniya.

Kamfanonin Afrika sun fara amincewa da tsarin hayar kayayyaki a matsayin wata hanyar sayen kayayyakin ICT, in ji darekta janar na Iway Afrika da ke Kenya, Kenneth Munyi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China