A jawabinsa yayin bikin sanya hannun wanda aka gudanar yayin taron kolin kamfanin reshen kudancin Afirka a birnin Johannesburg, shugaban sashen kasuwancin kamfanin Huawei mai kula da yankin kudancin Afirka Wilson Feng, ya ce, kamfanin ya kulla wannan yarjejeniya ce, ganin yadda kasashen na Afirja ke matukar bukatar wake-wake,da wasannin bidiyo na zamani.
Mr Feng ya ce, kamfaninsa zai yi aiki kafada da kafada da abokan huldansa na Afirka, ta yadda za su samar da yanayin da ya dace a wannan harka ba tare da gurbata muhalli ba.'
A nasa jawabin babban jami'in tsara shirye-shirye a hukumar watsa shirye-shirye ta Afirka ta kudu Siphumelele Zondi, ya ce, akwai bukatar masu fasaha a Afirka ta kudu su shiga a dama da su a fannin zamanintar da shirye-shirye, domin ta haka ne za a magance matsalar satar fasaha.
Alkaluma da kamfanin Huawei ya fitar sun nuna cewa, duk da karuwar da za a samu ta kashi 40 cikin 100 a kowace shekara a ayyukan ba da hidima na zamani nan da shekaru biyar masu zuwa, akwai babban gibi tsakanin bukatu da wakokin zamanin da ake samarwa.
Manufar taron kolin da kamfanin ya shirya ita ce, samar da kafar musayar ra'ayoyi, ta yadda za a inganta hadin gwiwa a fannin samar da wakoki ta hanyar fasahohin zamani a nahiyar Afirka. Kamfanonin da suka kulla yarjejeniyar da kamfanin na Huawei, sun hada da Spice Music,da Mtec, da CCA, da wasu masu sayar da wakoki na cikin gida.
Yanzu haka dai kamfanoni sama da 40 ne dai suka nuna sha'awarsu ta shiga wannan hadin gwiwa.(Ibrahim)