Kwamitin tattalin arziki na MDD na Afrika wato UNECA yana kokarin inganta karfin nahiyar ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen harhada bayanai yadda ya kamata, da kuma aiwatar da shawarwari, duk da cewar akwai ci gaba a karfin ajiye kididdgar game da nahiyar, tsarin kididdigar har yanzu bai cimma yadda ake bukata ba saboda matsalolin da ake fuskanta.
Kwamitin na UNECA ya ce, duk da hanyoyin sadarwa da watsa bayanai na zamani sun shafi kowane bangare na rayuwan dan adam da ya hada da tattara bayanai, nahiyar ta Afrika har yanzu tana fuskantar kalubale wajen tattara bayanai saboda rauni da take da shi a kayyakin zamani da kuma dogara da ta yi kan amfani da takardu.
Kwamitin ya shirya taron bita na yini hudu na yankuna da za'a tattauna kan yadda za'a yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani don harhada bayanai a ranar Talata a Adis Ababa na kasar Habasha.(Fatimah)