in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a birnin Baghdad
2017-02-18 13:05:17 cri
A Jiya Jumma'a ne babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya fidda wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da jerin hare-haren bomabomai da aka kai Baghdad babban birnin kasar Iraki.

Mataimakin kakakin MDD, Farhan Haq ne ya karanta sanarwar yayin taron manema labaran da aka saba yi.

Sanarwar ta ce, tuni kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi, ta sanar da daukar alhakin hare-haren na birnin Baghdad.

Haka zalika, Sanarwar ta ruwaito Mr. Guterres na yabawa al'ummomin kasar Iraki bisa kokarin da suke na yaki da yaduwar ta'addanci a kasar, inda ya ce MDD za ta ci gaba da taimakawa gwamnati da al'ummomin Iraki, wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, ta yadda za a kiyaye fahimtar juna ta hanyar hawan teburin neman sulhu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China