in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraqi ta aiwatar da hukuncin kisa ga mayakan kungiyar IS 36
2016-08-22 11:38:26 cri

Gidan talabijin na kasar Iraqi, ya ce hukumar shari'ar kasar ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa ga 'yan kungiyar IS 36 a jiya Lahadi 21 ga wata.

Gidan telibijin mallakar kasar ya bayyana cewa, wadannan mutane 36 suna da hannu kan kisa sojojin Iraqi 1700, yayin da IS ta kwace yankin Tikriti a watan Yuni na shekarar 2014. An aiwatar da hukuncin kisa ga wadannan fursunoni 36 ne a gidan kurkuku dake Nasiriya.

Tun dai cikin watan Yunin shekarar 2014 ne Iraqi ta kara tsunduma cikin mawuyacin hali na tsaro, inda kungiyar IS ta kwace wasu muhimman biranen kasar, ciki hadda Sumoer da Tikriti, kana IS ta tsare sojojin gwamnatin Iraqi su 1700, yayin da suke kokarin gudu daga sansanin soja dake karkarar Tikriti. Daga baya, IS ta gabatar da bidiyon kisan gillar da ta yi wa wadannan sojoji.

A shekarar bara kuma, dakarun gwamnatin Iraqin sun gano gawawwaki fiye da dari daya yayin da suka kwato birnin Tikriti. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China