Magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Larabar nan ya mika sakon murna ga Firaministan kasar Iraqi Haider al-Abadi game da nasarar sake karbe birnin Ramadi daga kungiyar ISIS na Iraqin da Syria.
Kamar yadda ofishin kakakin Majalissar ya bayyana, Mr. Ban ya taya murnar ne ta wayar tarhon da ya kira, inda ya lura da cewa, samar da 'yancin Ramadi wace nasara ce mai muhimmanci tare da jaddada bukatar daukar matakai na dawo da doka da oda da ma sauran ababen bukatu a garin, ta yadda wadanda suka rasa matsugunansu za su samu komawa gida.
Sai dai kuma Mr Ban ya nuna damuwarsa game da sace wadansu 'yan Qatar da ke kasar ta Iraqi da suka hada da yara kananan, yana mai kira ga Mr. al-Abadi da ya yi duk abin da ya kamata na ganin an tsirar da su cikin gaggawa kuma lafiya lau.
Bayan kwace mafi yawan birnin na Ramadi daga hannun kungiyar mayakan ISIS, al-Abadi ya tashi zuwa yammacin birnin na Ramadi a ranar Talata domin bikin wannan nasarar.(Fatimah Jibril)