in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 20 sun rasu sakamakon harin kunar bakin wake a Iraki
2016-07-08 13:35:46 cri
Wani jami'in tsaron kasar Iraki ya bayyana a yau Jumma'a cewa, an kai wani harin kunar bakin wake a safiyar yau a lardin Salahudin dake tsakiyar kasar Iraki, harin da ya haddasa rasuwar mutane 20, yayin da wasu 70 kuma suka jikkata.

Haka kuma, ya ce, wasu dakaru sun shiga wani wurin Ibadan 'yan shi'a da safiyar wannan rana, inda dakaru guda biyu suka tayar da boma-boman da ke jikinsu, yayin da ragowar maharani kuma suka kama wasu mutanen da suke aikin ziyara.

Rahotanni na cewa, an yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaron Iraki da maharani, inda aka halaka dukkan maharani kana aka ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Jami'in ya kuma bayyana cewa, fashewar da kuma musayar wuta tsakanin sassan biyu, sun haddasa mutuwar mutane a kalla 20 yayin da wasu 70 suka jikkata. Da alamun kungiyar IS ce ta shirya da kuma aiwatar da wannan hari, in ji shi.

Amma ya zuwa yanzu, babu wani mutum ko wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China