Wata sanarwar da jami'in rundunar hadin gwiwa Abdul-Amir Yarallah ya fitar, ta ce dakarun Iraqi sun kwace iko da kananan garuruwan Malayeen da Al-Bina al-Jahiz dake tsakiyar Mosul, inda suka daga totocin kasar a wasu gine-gine.
Yarallah ya ce wadannan ne yankunan tsakiyar Mosul da suka rage, wato yankin da aka fi sani da gabar kogin Tigris da ya raba birnin.
Ya kara da cewa, dakarun sun kuma kwace iko da babbar hanyar da ta hada birnin Mosul da lardin Dohuk, wanda wani sashe ne na yankin Kurdistan dake da kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai.
Da wannan nasarar, dakarun Iraqi sun kwace iko da dukkanin yankin gabashin Mosul, inda yankin Rashidiyah dake wajen arewacin birnin, ya kasance yanki daya tilo dake karkashin ikon kungiyar IS.
Masana sun ce da zarar dakarun sun kwace baki dayan gabashin Mosul, za su kaddamar da wani sabon yaki kan kungiyar a yankin yammacin birnin.( Fa'iza Mustapha)