Haka kuma, cikin sanarwar, bangarorin biyu sun jaddada cewa, ya kamata al'ummomin kasar Afghanistan su kasance a kan gaba kana su warware ricikin kasarsu da kansu ta hanyar siyasa. kana, a matsayinta na wakilan din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin da kasar Burtaniya za su ci gaba da nuna goyon baya ga gamayyar kasa da kasa domin taimaka wa rundunonin sojojin kasa ta Afghanistan cimma burinsu na shimfida zaman lafiya a kasar.
Bugu da kari, kasashen Sin da Burtaniya sun cimma daidaito na yin hadin gwiwa da gwamnatin kasar Afghanistan, domin taimaka wa kasar Afghanistan taya hukumominta da ababan more rayuwa ta hanyar hadin gwiwar masanan kasashen uku. (Maryam)