Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da bai wa gwamnatin kasar Afghanistan tallafi da goyon baya, a kokarin gaggauta wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasar.
A jiya Laraba ne dai kwamitin sulhun ya shirya wani taro kan batun Afghanistan, tare da zartas da wata sanarwar shugaba, inda ya kalubalanci sassa daban daban da su hada kai wajen samar wa jama'ar Afghanistan kyakkyawar makoma ta zaman lafiya da wadata.
A cikin jawabinsa a yayin taron, Wu Haitao ya ce, a Afghanistan sulhunta al'umma yana gaban komai. Kuma ya kamata sassa daban daban na kasar su mayar da makomar kasarsu, da kuma moriyar jama'arsu a gaban kome, su kuma koma ga teburin shawarwarin zaman lafiya cikin hanzari.
Kaza lika ya zama wajibi kasashen duniya su ci gaba da yin kokari, wajen goyon bayan aikin sulhu tsakanin dukkan bangarorin kasar ta Afghanistan, a karkashin shugabancin jama'ar kasar, ko a kai ga cimma nasarar sulhu a wannan kasa. (Tasallah Yuan)