in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya sanar da dakatar da shirin janye sojojin Amurka daga Afghanistan
2016-07-07 13:31:19 cri

A jiya Laraba, shugaban Amurka Barack Obama ya sanar da dakatar da shirin janye sojojin Amurkar daga kasar Afghanistan, inda ya bayyana cewa, za a kiyaye kasancewar sojojin Amurka kimanin 8400 a Afghanistan kafin wa'adin aikinsa ya cika a watan Janairun shekara mai zuwa.

Yayin da shugaba Obama ya gabatar da jawabi a jiya a fadar White House, ya bayyana cewa, har yanzu ba a samu yanayin tsaro yadda ya kamata a kasar Afghanistan ba, kuma sojojin Afghanistan ba su da karfi sosai, don haka ci gaba da jibge sojojin Amurkar zai iya ba da taimako wajen habakar sojojin Afghanistan.

Bugu da kari, Shugaba Obama ya ce, ya tsai da wannan kuduri na dakatar da shirin janye sojojin ne bayan da ya saurari shawarar sojojin Amurkar, da kuma yin tattaunawa tare da hukumar tsaron kasar. Wannan sabon shirin zai iya aza harsashi ga mai gadonsa wajen taimakawa Afghanistan don samun dauwamammen ci gaba, baya ga kiyaye karfi wajen yaki da ta'addanci yadda ya kamata.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China