Hakan yana nuna alamar cewa, a karshe an kaddamar da wannan muhimmin aiki bayan wahalhalu da aka fuska a baya game da kokarin bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Birtaniya.
A sa'i daya kuma, wannan wata dama ce ta amfani da sabbin fasahohin samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya na Sin a ketare.
Bayan da ta kama aikinta na tsawon makwanni, firaministar kasar Birtaniya, madam Theresa Mary May ta kuduri aniyyar sake binciken aikin na Hinkley Point. Wasu kafofin yada labarai na Birtaniya suna zaton ganin cewa, yanzu gwamnatin Birtaniya ta kartata harkokinta na zuba jari zuwa kasar Sin. A ranar 15 ga watan Satumba ne, gwamnatin Birtaniya ta ba da sanarwar zartas da wannan aiki na karshe.(Fatima)