in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Birtaniya
2016-04-10 13:08:12 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaran aikinsa na kasar Birtaniya Philip Hammond a jiya ranar 9 ga wata a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da Birtaniya sun yi amfani da damar sakamakon ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Birtaniya, don zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. Yana fatan bangarorin biyu za su yi kokari tare da kiyaye yin mu'amala a tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da kara fahimtar juna, da kuma tabbatar da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a wannan yanayi mai kyau.

Hammond ya bayyana cewa, kasar Birtaniya ta dora muhimmanci ga yanayi mai kyau na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya, kuma tana fatan ci gaba da yin kokari tare da Sin don aiwatar da ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da inganta hadin gwiwarsu kan harkokin kasa da kasa.

Wang Yi ya bayyana ra'ayin Sin kan batun Hongkong da na tekun Nanhai ga Hammond. Wang Yi ya bayyana cewa, harkokin Hongkong harkokin cikin gida na kasar Sin ne. Gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar kasa daya, da tsarin mulki iri biyu da 'yan Hongkong suke bi wajen gudanar da harkokin Hongkong. Sin ta nuna yabo ga kasar Birtaniya da ta nuna kin amincewa da ra'ayin cin 'yancin Hongkong. Wang Yi ya yi nuni da cewa, Sin tana fatan Birtaniya za ta dauki matsayin da ya dace kuma bisa adalci kan batun tekun Nanhai. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China