in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Birtaniya sun bayar da sanarwa game da batun Syria
2016-01-06 10:38:34 cri
Kasashen Sin da Birtaniya sun fidda sanarwar hadin gwiwa game da batun kasar Syria. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyanawa 'yan jarida hakan, bayan ganawar sa da ministan harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond a nan birnin Beijing a jiya Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa, Sin da Birtaniya sun damu matuka game da mawuyacin hali, da halin jin kai, da tashe-tashen hankula, da tasirin ta'addanci da rikicin dake addabar kasar ta Syria.

Har wa yau sanarwar ta yi nuni da cewa, a matsayin su na kasashe mambobin dindindin a kwamitin sulhu na MDD, Sin da Birtaniya sun jefa kuri'ar goyon baya ga kuduri mai lamba 2254, da kwamitin sulhun ya gabatar a kwanakin baya. Kaza lika kasashen biyu za su ci gaba da shiga ayyukan rukunin aiki na kasa da kasa, da kokari tare da kasashen dake yankin, don tabbatar da samar da yanayin wucin gaba a fannin siyasa a kasar Syria, wato baiwa 'yan Syria damar mallakar ikon kasar su, kudurin da aka gabatar da shi a cikin sanarwar Geneva.

Hakan a cewar sanarwar zai taimakawa wajen kawo karshen yake-yake, da kafa hukumar wucin gadi mai samun cikakken iko bisa tushen amincewar bangarori daban daban.

Sanarwar ta kara da cewa, Sin da Birtaniya sun amince da yaki da ta'addanci, yayin da ake warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa. Sun kuma jaddada cewa, hanyoyin dakile ta'addanci sun kasance muhimmai wajen kaucewa barazana mafi tsanani a duniya a fannin kiyaye zaman lafiya. Don haka kasashen biyu za su ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin yaki da ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya, da arewacin Afirka, da sauran yankuna ciki har da kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar Syria. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China