A jiya Alhamis 10 ga watan nan ne mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao, ya bayyana wa taron tattauna batutuwan 'yan sandan kiyaye zaman lafiya, wanda kwamitin sulhu na MDD ya kira cewa, ya kamata a danka cikakken izni ga 'yan sandan kiyaye zaman lafiya, bisa bukatun kasashen da abin ya shafa, da kuma halin da ake ciki a kasashen da dai sauransu, ta yadda 'yan sandan za su samu zarafin aiwatar da ayyukansu, da kuma mai da hankali kan harkoki mafiya muhimmanci yadda ya kamata.
Ya ce, kasar Sin na kan gaba wajen aikewa da 'yan sandan kiyaye zaman lafiya, cikin mambobin kwamitin sulhu na MDD, kuma a halin yanzu, tana da 'yan sandan kiyaye zaman lafiya sama da 170 dake aiki cikin tawagogin musamman na MDD a kasashen Liberia, da Sudan ta Kudu da dai sauran kasashe. (Maryam)