A wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, kwamitin majalisar dinkin duniyar ya bukaci gwamnatin kasar Mali da ta hanzarta gudanar da bincike domin gano wadanda suka aika wannan danyen aiki domin hukunta su.
Harin wanda ya faru a ranar Lahadi da ta gabata a kusa da Douentza a yankin Mopti dake tsakiyar Mali, ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kasar Mali biyu, da kuma jami'in wanzar da zaman lafiya guda, dan kasar Togo. Kana an jikkata wasu jami'an wanzar da zaman lafiyar 7, dake aiki karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD wato MINUSMA. (Ahmad Fagam)