Ranar 25 ga wata, Yang Jiechi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin ya halarci liyafar murnar cika shekaru 45 da MDD ta maido wa jamhuriyar jama'ar Sin halatattun hakkokinta.
A cikin jawabinsa a yayin liyafar, Yang Jiechi ya ce, shekaru 45 ke nan da suka gabata, babban taron MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2758, inda aka tsai da kudurin maidowa jamhuriyar jama'ar Sin halatattun hakkokinta, lamari ne dake da matukar muhimmanci a tarihi, wanda ya shaida cewa MDD ya kyautata wakilcinta da martabarta sosai, karfin duniya na kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa ya samu ingantuwa, kana kasar Sin ta shiga sabon zamani a harkokin jakadanci. A cikin shekaru 45 da suka wuce, kullum kasar Sin na himmantuwa wajen wanzar da zaman lafiya a duniya, da ba da gudummowa wajen ci gaban duniya, da kiyaye dokokin kasa da kasa, da goyon bayan al'amurran MDD. Kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, da samun bunkasuwa, da kuma yin hadin gwiwa da kasashen duniya. Tana son yin kokari tare da MDD da sauran kasashen duniya wajen kara azama kan zaman lafiya da ci gaban rayuwar dan Adam. (Tasallah Yuan)