Haka kuma, Mr.Geng ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce zaunanniyar wakiliya ta kwamitin tsaron MDD, kana, mambar masu daukar alhakin gamayyar kasa da kasa, za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan babban magatakardan MDD yadda ya kamata.
A ranar ga wannan wata ne 13 babban taron MDD karo na 71, ya zartas da kuduri cewa, tsohon firaministan kasar Portugal, kana tsohon babban wakilin MDD dake kula da harkokin 'yan gudun hijira Antonio Guterres ya kasance sabon babban magatakardan MDD a hukumance. (Maryam)