in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya yi kiran samar da zaman lafiya da ci gaba
2016-10-25 09:24:43 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa majalisar a kokarin da take yi na ci gaba da samar da zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa da kuma kare hakkin bil-Adam.

Mr. Ban ya yi wadannan kalamai ne a yayin bikin ranar da aka kafa MDD a shekarar 1945.

Bikin ranar MDD na wannan shekara ya zo ne a dai-dai lokacin da babban sakataren majalisar na 9 yake shirin karbar jagorancin majalisar.

Ban Ki-moon ya kuma mika godiyarsa dangane da irin goyon bayan da jama'a a fadin duniya suka ba shi yayin da yake shugabancin majalisar. Kana ya bukaci a baiwa wanda zai gaje shi Antonio Guterres irin wannan goyon baya, ta yadda zai samu nasarar ci gaba da kokarin majalisar na samar da zaman lafiya, ci gaba mai dorewa da kuma kare hakkin bil-Adama a duniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China