Kafin gudanarwar da taron, Ban Ki-moon ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, a wannan rana ne aka bude wani sabon shafi na tarihin dan Adam kan yaki da sauyin yanayi a duniya, yarjejeniyar Paris ta fara aiki a hukunce.
Kaza lika ya ce, a ranar 7 ga watan nan da muke ciki, za a yi taron masu kulla yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 22 a birnin Marrakech na kasar Morocco, kuma babban kalubale da ake fuskanta shi ne, yadda za a ciyar da yarjejeniyar Paris gaba, shi ya sa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su karfafa aniyarsu wajen gina wata duniya mai tsaro da kuma mai dauwamammen ci gaba bisa fasahohin da za su dace da halin da ake ciki.
Bugu da kari, shugaban babban taron MDD karo na 71 Peter Thomsen, ya fidda wata sanarwa a wannan rana inda ya bayyana cewa, fara aiki da yarjejeniyar Paris ya kasance muhimmin matakin da aka dauka wajen fuskantar sauyin yanayi a duniya, wanda ya kuma ba da tabbaci wajen warware matsalar da abin ya shafa. (Maryam)