in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taya MDD murnar cika shekaru 30 da kafa cibiyar shimfida zaman lafiya da kwance damarar soja
2016-10-28 10:10:05 cri

Shekarar 2016 shekara ce da cika shekaru 30 da kafa cibiyar shimfida zaman lafiya da kwance damarar soja ta MDD. Bisa gayyatar mataimakin babban magatakardan MDD kuma wakili mai kula da harkokin kwance damara Kim Won Soo, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya gabatar da jawabi ta bidiyo kan wannan batu.

A jawabinsa, Mr. Liu ya taya MDD murnar cika shekaru 30 da kafa cibiyar shimfida zaman lafiya da kwance damara. Gudanar da ayyukan kwance damarar soja da kayyade yawan sojoji a wurare daban daban bisa la'akari da yanayinsu zai kyautata tsaron kasashe membobi, kuma zai rage yawan rikice-rikice a shiyyoyi daban daban, tare da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon da mataimakinsa Kim Won Soo da zaunannan wakilan kasashen Jamus da Jamaica da kuma Najeriya dake MDD su ma sun gabatar da jawabai ta bidiyo bisa gayyatar da aka yi musu, inda suka yaba da rawar da wannan cibiya ta taka a cikin shekaru 30 da suka gabata, kana suka yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da gudanar da ayyukan kwance damara.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China