in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin sun gana da shugaban jamhuriyar Congo
2016-07-06 10:40:57 cri
Jiya Litinin 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na jamhuriyar kasar Congo Denis Sassou Nguesso a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijng.

A yayin ganawar shugabannin biyu, sun tsai da kudurin daga dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu zuwa iri na manyan tsare-tsare, domin aiwatar da sakamakon taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, tare da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da jamhuriyar Congo bisa dukkan fannoni, ta yadda al'ummomin kasashen biyu za su samu moriya daga wajen yadda ya kamata.

Shugaba Xi Jinping ya ce, ya kamata a zurfafa fahimtar juna a tsakanin kasar Sin da jamhuriyar kasar Congo a fannin harkokin siyasa, a sa'i daya kuma, a raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, yayin da ake neman dauwamemmen ci gaba a wannan fanni, kana a karfafa hadin gwiwa da shawarwari dake tsakanin gwamnatoci, jam'iyyu masu mulki, hukumomin kafa dokoki da kuma kananan gwamnatoci na kasashen biyu, lamarin da zai karfafa fahimtar juna a fannin siyasa a tsakanin Sin da jamhuriyar Congo, tare da inganta huldar abokantaka a tsakaninsu cikin dogon lokaci.

Kaza lika, Xi Jinping ya ce, ya kamata kasashen biyu su ciyar da hadin gwiwar dake tsakninsu gaba domin cimma moriyar juna, da kuma neman ci gaba cikin hadin gwiwa, kasar Sin tana son taimaka wa kasar Congo wajen bunkasa yankin musamman na tattalin arziki dake birnin Pointe-Noire na kasar, kuma bisa bunkasuwar wannan yanki, za a iya habaka hadin gwiwar kasashen biyu a fannoni masana'antu da makamashi, lamarin da zai ba da gudummawa matuka wajen raya fasahohin zamani na jamhuriyar kasar Congo a fannonin masana'antu da ayyukan gona, yayin da kuma samun bunkasuwar tattalin arziki daga duk fannoni, da kuma cimma dauwamammen ci gaba bisa karfin kanta.

A nasa bangare kuma, shugaban jamhuriyar kasar Congo Denis Sassou Nguesso ya taya wa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin murnar cikon shekaru 95 da kafuwarta, sa'an nan, ya bayyana cewa, ana tafiyar da dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Congo yadda ya kamata, har an samu babban sakamako da dama a fannonin ginawar ababen more rayuwa, ayyukan sandarwa, samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da kuma kiwon lafiya da dai sauransu.

Haka kuma, ya ce, kasarsa tana son ci gaba da habaka hadin gwiwar kasashen biyu wajen raya yankin musamman na tattalin arziki da samar da kayayyaki da makamashi, ciniki, da al'adu da dai sauransu, tana kuma sa ran kamfanonin kasar Sin za su kara zuba jari a kasarsa.

A yayin da yake tsokaci kan batun tekun kudancin kasar Sin kuma, Mr. Nguesso ya bayyana cewa, jamhuriyar kasar Congo ta amince da matsayin kasar Sin kan wannan batu, za ta kuma ci gaba da ba da goyon baya ga Sin cikin harkokin kasa da kasa.

Bugu da kari, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa ta Sin Zhang Dejiang ya kuma gana da Mr. Nguesso a babban dakin taron jama'a a wannan rana, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Congo domin aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka guda goma a kasar tun da wur wuri, ta yadda za a inganta hadin gwiwar kasashen biyu yadda ya kamata da kuma ba da karin tallafi ga al'ummomin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China