in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na ketare sun mai da hankali kan muhimmin jawabin shugaba Xi na ranar daya ga watan Yuli
2016-07-04 11:13:12 cri

A ranar daya ga wata, babban sakataren kwamtin tsakiyar JKS Xi Jinping ya yi muhimmin jawabi a gun babban taron murnar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Kafofin yada labaru na ketare sun mai da hankali sosai kan jawabin, tare da gabatar da labarai dangane da abubuwan dake shafar tsayawa tsayin daka kan bin tunanin Markisanci, da kulawa da harkokin JKS yadda ya kamata, da ikon mallakar cikakken yankin kasa da sauransu.

Kamfanin dillancin labaru na Associated Press AP ya mai da hankali sosai kan maganar da shugaba Xi ya yi ta cewar, 'tunanin Markisanci ya zama babban tushe na kafa JKS da kasar Sin, idan an yi watsi da shi, JKS za ta rasa hanyar da za ta bi a nan gaba'. Game da wannan, kamfanin dillancin labaru na AP ya yi sharhi cewa, jawabinsa ya bayyana cewa, shugaba Xi yana dora muhimmanci sosai kan kara kulawa da abubuwan dake tunanin jama'a da harkokin JKS.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, dole ne mu yi tsaya tsayin daka, ba za mu yi hakuri kan kowane laifi ba, mu yi iyakacin kokari domin yin bincike kan batutuwa da yaki da cin hanci da rashawa, da zummar kawar da masu cin hanci da rashawa daga JKS. Game da wannan batu, kamfanin dillancin labaru na Reuters ya yi sharhi cewa, jawabin nasa ya jaddada cewa, yanzu cin hanci da rashawa ya fi yin barazana ga JKS.

Kamfanin dillancin labaru na Interfax na Rasha ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping a cikin 'yan shekarun da suka wuce, an yi kokarin yaki da cin hanci da rashawa a cikin JKS da gwamnatoci da rundunar soja, hakan ya kara kwarin gwiwar jama'ar kasar ga JKS, tare da sa kaimi ga yin kwaskwarima a kasar. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China