Kudaden ketare da Sin ta yi amfani da su cikin watanni biyar da suka gabata ya wuce dallar Amurka biliyan 50
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fidda wani rahoto a jiya Lahadi, wanda ke cewa, a cikin watanni biyar da suka gabata na wannan shekara, jarin da aka zuba a kasar Sin daga kasashen ketare ya yi ta karuwa, inda gaba daya, Sin ta yi amfani da jarin ketare har dallar Amurka biliyan 54.19, adadin da ya karu da kashi 3.8 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar da ta gabata, haka kuma, adadin sabbabin kamfanonin dake samun jarin 'yan kasuwar ketare shi ma ya ci gaba da karuwa.
Bugu da kari kuma, bayanai na nuna cewa, an fi zuba jari a bangare sana'o'in ba da hidima ta fuskar fasahar zamani. A sa'i daya kuma, adadin jarin da aka zuba a fannin kera kayayyaki ya ragu sannu a hanakali, sabili da haka ne a nan gaba kuma, ma'aikatar kasuwancin kasar ta Sin za ta dauki matakan da za su dace wajen tabbatar da adadin jarin da za a zuba a fannin kera kayayyaki.
Haka zalika kuma, yankin dake yammacin kasar ta Sin ya fi samun jari daga ketare, kana, adadin jarin da aka zuba a yankin dake gabashin kasar yana cikin yanayi mai kyau. (Maryam)