Masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki a Najeriya, na gudanar da taron warware matsalolin da suka dabaibaye sashen, a gabar da kasar ke ci gaba da fuskantar karyewar farashin danyan mai, da karancin kudaden shigar gwamnati, da kuma ayyukan tsagerun Niger Delta.
Mashirya taron sun bayyana cewa, makasudin haduwar shi ne tattara dabaru daga masana a fannin tattalin arziki, domin tallafawa gwamnati wajen gano karin hanyoyin warware matsalolin tattalin arzikin kasar.
Da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, daraktan sashen manufofin kudi na babban bankin Najeriya CBN Moses Tule, ya ce, yayin taron za a nazarcin daukacin sassa masu nasaba da kalubalen da tattalin arzikin Najeriyar ke fuskanta.
Kakakin majalissar wakilan kasar Yakubu Dogara, da shuwagabannin masana'antu, da wakilan gwamnati tare da jami'an babban bankin kasar na cikin mahalarta taron.(Saminu)