in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen waje a watanni 11 na wannan shekara ya karu da kashi 16 cikin dari
2015-12-16 11:18:48 cri

Jami'in sashen zuba jari da hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen waje na ma'aikatar cinikin kasar Sin ya bayyana a jiya Litinin cewa, a watanni 11 na farkon wannan shekara, yawan jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen waje ya kai dalar Amurka biliyan 104.13, wanda ya karu da kashi 16 cikin dari bisa makamacin lokacin na bara.

Jami'i ya ce, kasar Sin ta zuba jari a kasashen waje a dukkan fannonin da ke da nasaba da tattalin arziki da zaman takewar al'umma. Yawan jari da kasar Sin ta zuba a bangaren sana'o'in kera kayayyaki ya karu da kashi 95.4 cikin dari, daga cikinsu, ciki kuwa yawan jarin da aka zuba a bangaren sana'ar kera na'urori ya karu da kashi 117.3 cikin dari.

Ya ce, kamar yadda aka yi hasashe yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje zai karu fiye da kashi 10 cikin dari a wannan shekara. A watanni 11 na farkon wannan shekara, harkokin zuba jari da hadin gwiwa tare da kasashen waje da kasar Sin ke gudanarwa sun samu kyautatuwa karkashin shirin nan na ziri daya da hanya daya, kana hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen waje a fannin samar da kayayyaki shi ma ya karu cikin sauri.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China