Jakadan kasar Kenya dake kasar Sin Michael Kinyanjui ya ce, kasar sa ta dauki matakai da dama domin sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar, bayan kasashen biyu sun daga dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. Ayyukan noma da kirkire-kirkire na fuskar makoma mai kyau, kasar tana kuma sa ran raya harkokin masana'antunta.
Kaza lika, a halin yanzu, kamfanonin kasar Sin sama da dubu uku suna zuba jari a nahiyar Afirka, tafiya-tafiyar mutane a tsakanin Sin da Afirka ya kai sama da miliyan 3.6 a shekarar 2014, haka kuma, harkokin da kamfanonin kasar Sin suka zuba jari a Afirka sun hada da makamashi, ma'adinai, kayayyakin gine-gine da dai sauransu, gaba daya sun zuba jari sama da dallar Amurka biliyan 4.7 a nahiyar, lamarin da ya kasance babban bunkasuwar kamfanonin Sin a Afirka. (Maryam)