Mr. Zhang ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da aka gudanar a jiya Litinin, dangane da taron shawarwari kan manyan tsare-tsare, da harkokin tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka a karo na takwas.
Ya ce, a fannin ciniki, ya kamata kasashen biyu su kauracewa tsarin baiwa cinikayya kariya, sa'an nan, kasar Amurka ta dauki matakan da za su dace wajen sassauta yanayin fitar da hajojin ta zuwa kasar Sin.
Haka kuma, da yake tsokaci kan harkar zuba jari, Mr. Zhang ya ce, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da maimaita wannan yanayi mai kyau na habaka harkokin zuba jari, yayin da ake ciyar da shawarwarin yarjejeniyar zuba jari gaba a tsakanin bangarorin biyu. A cewar sa hakan ya dace da moriyar Sin da Amurka.
Kaza lika kasar Sin na fatan Amurka za ta samar da yanayin adalci ga kamfanonin kasar Sin, a yayin da take gudanar da aikin binciken yanayin hadewar kamfanoni. (Maryam)