A cewar rahoton, kasashe ko yankuna 10 da suka fi jawo jarin kasashen waje a duniya a shekarar 2014 sun hada da Sin, yankin Hongkong, Amurka, Britaniya, Singapore, Brazil, Canada, Australia, Indiya da kuma Netherlands.
Shugaban sashen kula da harkokin zuba jari da kamfanoni na hukumar Zhan Xiaoning ya bayyana cewa, wannan rahoto ya shaida cewa, Sin tana daya daga cikin manyan kasashe ko yankunan da suka fi jawo hankulan masu sha'awar zuba jari a duniya, kana Sin ta kara taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin zuba jari a duniya. (Zainab)