Bankin duniya da bankin raya kasar Sin sun yi kira da a kafa kawancen masana mai kula da harkokin zuba jari a Afrika a gun taron farko na dandalin tattaunawa kan zuba jari a Afrika da aka kammala shi a jiya Laraba a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, a kokarin yada fifikon wadannan manyan bankunan biyu wajen ingiza ci gaban Afrika, ta yadda za a kawo moriyar kasar Sin da kasashen Afrika tare.
Mataimakin shugaban bankin raya kasar Sin Yuan Li ya ce, makasudin kafa kawancen masana mai kula da harkokin zuba jari a Afrika shi ne ba da shawarwari kan manufofin zuba jari a Afrika ga dandalin tattaunawa a fannin.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban bankin duniya mai kula da harkokin Afrika Makhtar Diop ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afrika su ne muhimman abokan juna, don haka ya yi imani da cewa, dandalin tattaunawar zai inganta bunkasuwar kasashen Afrika, baya ga kara azama ga kasar Sin da kasashen Afrika don moriyar juna da samun nasara tare.
A wannan rana kuma, bankin raya kasar Sin ya kulla yarjejeniya tare da kungiyar raya masana'antu ta MDD, idan suka yi alkawarin karfafa hadin gwiwarsu da kuma taimakawa juna wajen gudanar da ayyuka a Afrika da kuma kasashen dake da nasaba da shirin "ziri daya da hanya daya".
Bankin duniya da kasar Sin da kuma kasar Habasha ne suka jagoranci wannan taron farko na dandalin tattaunawa kan zuba jari a Afrika. (Lami)