in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kyautata ayyukan kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, in ji ministan wajen Sin
2016-05-25 10:48:55 cri
Jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, wanda aka gudana a birnin Tashkent na kasar Uzbekistan.

A yayin taron, Mr. Wang ya gabatar da jawabi, yana mai cewa, shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 15 da kafuwar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, haka kuma, cikin wadannan shekaru 15 da suka gabata, an sami sakamako da dama a fannoni daban daban, a fannin hadin gwiwar mambobin kungiyar, lamarin da ya ba da gudummawa matuka wajen ciyar da bunkasuwa da zaman karko na yankin gaba.

Daga bisani kuma Mr. Wang ya ba da shawarwari guda biyar, game da yadda za a ci gaba da kyautata ayyukan kungiyar yadda ya kamata. Ya ce da farko ya kamata a karfafa fahimtar siyasa da hadin gwiwar dake tsakanin mambobin kungiyar. Sai na biyu a dauki matakan kandagarkin wasu matsalolin tsaro, wadanda mai iyuwa ne za a iya gamuwa da su. Sa'annan na uku a aiwatar da ayyuka ta hanyoyin da za su dace, yayin da kuma ake habaka hadin gwiwa yadda ya kamata. Daga karshe na hudu ya kamata a kyautata tsarin kungiyar, tare da kuma neman karin ma'aikata, baya ga karfafa mu'amalar al'adun dake tsakanin sassan, ta yadda za a iya kyautata zumuncin dake tsakanin al'ummomin mambobin kungiyar.

A daya bangaren kuma, ya ce, kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da mambobin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai bisa fannoni daban daban, don haka ne ma take fatan aiwatar da harkokin taron Tashkent yadda ya kamata, ta yadda za a iya karfafa ayyukan kungiyar a nan gaba, yayin da ake ba da karin tallafi ga yankin, har ma ga al'ummoni mambobin kasashen kungiyar baki daya.

Bugu da kari, wasu ministocin harkokin wajen mambobin kasashen kungiyar sun nuna cewa, duba da sabon yanayin da ake fuskanta a halin yanzu, ya kamata mambobin kungiyar su karfafa hadin gwiwarsu a fannonin tsaro, da tattalin arziki da kuma musayar al'adu, ta yadda za a iya zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomi mambobin kasashen kungiyar.

Haka kuma, mambobin kasashen suna goyon bayan kungiyar wajen ba da gudummawa kan aikin hada shirin zirin tattalin arzikin na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, da shirin hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin Asiya ta Turai tare, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar Asiya da Turai gaba cikin hadin gwiwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China