Yawan jarin da Sin ta zuba ga kasashen waje kai tsaye ya karu da kashi 16.5 cikin dari
Shugaban sashen kula da zuba jari da hadin gwiwar tattalin arziki na ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin Zhou Liujun ya bayyana a ranar alhamis 15 ga wata cewa, yawan jarin da Sin ta zuba ga kasashen waje kai tsaye da bai shafi hada-hadar kudi ba, a watanni 9 na farkon bana ya kai dala biliyan 87.3, wanda ya karu da kashi 16.5 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Hadin gwiwa da zuba jari da Sin ta yi a kasashen waje ya ci gaba da samun karuwa cikin sauri.
An ce, a yayin da ake zuba jari da hadin gwiwa a kasashen waje, an kara yin hadewar masana'antu ta hanyar zuba jari. A watannin 9, kamfanonin Sin ta gudanar da ayyukan hadewar masana'antu 324 wadanda suka shafi kasashe da yankuna 50, kuma yawan kudin da abin ya shafa ya kai dala biliyan 20.18. hakazalika kuma, ayyukan sun shafi fannoni 18 ciki har da kera kayayyaki, sadarwa da dai sauransu. (Zainab)