in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kasashen Afirka sun amince da dakile cinikayyar hauren giwa
2016-04-19 20:46:26 cri
Wasu kasashen Afirka sun sa hannu kan takardar yarjejeniyar kare giwaye, a yayin taron ministoci kan harkokin muhalli karo na shida dake gudana a birnin Alkahira na kasar Masar, inda suka amince da daukar matakan da suka kamata na hana cinikin hauren giwa.

An fara taron ne dai a ranar 16 ga watan nan da muke ciki, za kuma a rufe shi a yau Talata 19 ga wata. Ministocin dake kula da harkokin muhalli da wasu jami'an da abin ya shafa, wadanda suka zo daga kasashen Afirka guda 54 na cikin mahalarta wannan taro. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China