Bugu da kari, Zhou Xiaochuan ya bayyana cewa, yanayin tattalin arzikin kasar Sin ya gudana cikin kyakkyawan tsari, inda a shekarar 2015, duk da yake an gamu da yanayin raguwar ciniki a kasuwannin duniya, da kuma tabarbarewar sha'anin kudin kasa da kasa, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da samun karuwa ta kaso 6.9 bisa dari, lamarin da ya kasance ci gaba ne a tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. (Maryam)