in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kafa wani kawance domin bunkasa masana'antunta
2016-02-02 20:46:50 cri

Kwanan baya, kasar Sin ta sake daukar wani mataki domin hade masana'antu da yanar gizo ta Internet da kuma yadda za su tallata kansu domin samun bunkasuwa.

Kamfanonin masana'antu, harkar sadarwa, harkokin yanar gizo, jami'o'i, da kamfanonin jarin waje guda 143 sun kafa wani kawance, a kokarin lalubo bakin zaren raya masana'antu a kasar Sin ta hanyar yanar gizo.

Masana suna ganin cewa, wannan wata dama ce ta yadda masana'antu za su tallata kansu da kuma hajojin da suke samarwa. Bugu da kari, zai warware matsalolin fasaha, ka'idojin kafa masana'anta, yin gwaje-gwaje da dai sauransu. Masana'antu da yanar gizo za su kasance sabuwar jagora wajen hada fasahar bayanai da masana'antu tare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China