Wannan mataki da babban bankin kasar ta Sin ya dauka, ta sa a halin yanzu, ake nuna damuwa kan ko darajar kudin Sin za ta ci gaba da raguwa ko a'a.
Kakakin babban bankin kasar ta Sin ya fidda wata sanarwa a yau dangane da lamarin, inda ya jaddada cewa, babu abin da za a ganin ci gaban raguwar darajar kudin Sin a nan kasar.
Kuma dalilan da ya sa ya bayyana hakan, su ne, na farko, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na kan gaba a duniya, na biyu, ana ci gaba da samun rarar kudi a wasu manyan fannoni, na uku, kudin kasar na ci gaba da samun saurin bunkasuwa a kasuwannin duniya kana ana ci gaba da samun karuwar kasuwannin hada-hadar kudin kasar a waje a 'yan shekarun nan, na hudu shi ne, yadda darajar kudin Amurka ke karuwa za ta ragu, na biyar shi ne, akwai isassun kudaden musaya da aka adana a nan kasar Sin, kuma harkokin kudi da kuma tsarin sha'anin kudin kasar na cikin yanayi mai kyau. (Maryam)