Mr. Udoma wanda ke wannan tsokaci yayin zantawar sa da 'yan tawagar bankin habaka ci gaban Afirka na AfDB, ya ce duk da kasancewar karyewar farashin man ya haifar da gibin kusan dalar Amurka miliyan 143.9 ya zuwa watan Disambar da ya gabata, a hannu guda sauye-sauyen da gwamnatin kasar mai ci ke aiwatarwa, da manufofin fadada hanyoyin samar da kudaden shiga, zai bada damar maida hankali ga sauran fannonin da ba na mai ba. Ya ce daukar wannan mataki zai samar da kimanin dala biliyan 30.3, na kudaden aiwatar da kasafin kudin.
Cikin matakan da gwamnati ke dauka domin rage tasirin faduwar farashin mai, akwai toshe hanyoyin barnata kudaden hukuma, da yaki da cin hanci da rashawa tare da sa kaimi ga tattara haraji.
Minista Udoma ya kara da cewa sakamakon matsalolin da Najeriya ke fuskanta na tattalin arziki, kamar raguwar darajar kudinta, da tabarbarewar manyan ababen more rayuwa, da wawashe baitilmali da wasu jami'ai suka yi, ya tilastawa gwamnatin mai ci kara azama wajen aiwatar da sauye-sauye, tare da neman hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki ciki hadda bankin na AfDB, domin samun rancen kudi har dalar Amurka biliyan 9.02, kudaden da ake fatan amfani da su wajen aiwatar da manyan ayyukan raya kasa.