Bisa labarin da shafuffukan internet na jaridar Wall Street Journal da ake bugawa cikin Sinanci, an ce, nan ba da dadewa ba, kudin Sin RMB zai zama daya daga cikin manyan kudade 10 a fadin duniya, da ake amfani da su wajen sayayya, kuma wannan ya nuna cewa, kudin Sin ya taka muhimmiyar rawa a fagen habakar tattalin arzikin duniya.
Ko da yake, yawan kason da ake amfani da RMB wajen sayen kayayyaki ya kai kashi 0.87 cikin 100 a kasuwannin duniya, akwai bambanci sosai tsakanin kudin Sin da Kudaden Dollar da na EURO, amma idan kasar Sin ta shiga cikin jerin manyan kudade 10 a kasashen duniya, hakan zai haifar da ma'anar musamman gare ta.(Bako)