Da take karin haske ga manema labarai ta shafin yanar gizo Christine Lagarde, ta ce, kasar Sin tana gudanar da gagarumin sauye sauye a sha'anin tattalin arzikinta, amma ba za ta fada cikin mawuyacin hali ba.
Lagarde ta ce, duk wani matsi da tsanani kasar Sin zata iya jurewa, kuma zata iya aiwatar da garam bawul a sha'anin tattalin arzikinta. Sannan ta bukaci kasar Sin data kara kaimi wajen inganta manufofinta na kasuwanci da suka hada da gyare-gyaren tsarin kamfanonin mallakar gwamnati.
Tunda farko jami'ar ta IMF ta fada a yayin wani jawabi a jami'ar Maryland cewar, tafiyar hawainiyar da kasar Sin ke fuskantar za ta iya fantsama ga sha'anin cinikayya da duniya kuma za ta rage bukatar da ake da ita na kayayyyaki, amma a nan gaba za'a samar da daidaito daga fanin zuba jari zuwa ga ayyuka na hidima da kuma bukatu na cikin gida, ta haka za a iya samar da gagarumin ci gaba ga kasar Sin dama duniya baki daya.(Ahmad Fagam)