Kamar yadda wani masani, Jonathan Stichbury Shugaban kamfanin Pine Bridges Investment dake bada shawarwari akan harkokin kudi da tattalin arzikin dukiya, yayi ma Xinhua bayani, yace duk da maganar da ake na tafiyar hawainiyar tattalin arzikin kasar Sin, kashi 6.9% na karuwar shi da kasar ta samu har yanzu shi ne akan gaba a yankin Asiya bisa ga matakin yankuna.
Raguwar shi a bangarorin masana'antu da sarrafa kayyaki tare da batutuwan samar da wasu kayayyaki da yawa fiye da kima, shi ne ake ta bayani akai. Bangaren sayayya da hidimomi na tattalin arzikin, duk da hakan suna cigaba a hankali kuma hidimomi a yanzu sun yi sama da kashi 50% na mizanin GDP na kasar Sin.
Mr. Stichbury yayi bayanin cewar cigaban tattalin arzikin Afrika ana sa ran ya karu zuwa kashi 4.4% a wannan shekara daga kashi 3.7% na shekarar bara . wannan inji shi ya biyo bayan karuwar zuba jari daga wajen al'umma, cigaban samar da hidimomi da kuma karuwan huldar ciniki da kasar ta Sin.(Fatimah Jibril)