in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta ci gaba da sassauta takunkumin da ta saka wa Cuba
2016-01-27 10:54:33 cri
Ma'aikatar kudi da ma'aikatar kasuwanci a Amurka sun sanar a jiya cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da sassauta takunkumin da ta sanya wa kasar Cuba a fannonin tafiye-tafiye da fitar da hajojinta zuwa kasar .

Rahotanni daga ma'aikatar kudi ta kasar Amurka na nuna cewa, Amurka za ta cire takunkumin biyan kudi da harkokin kudi da ta kakabawa kasar ta Cuba kamar yadda sabbin ka'idojin suka tanada game da fitar da hajojin daga kasar Cuba.

Ban da haka kuma, kasar Amurka za ta ba da tallafi ga wadanda aka amince da su wajen yin tafiye-tafiye zuwa kasar Cuba.

Haka kuma, sakataren kudin kasar Amurka Jacob J.Lew ya bayyana a wannan rana cewa, wadannan sabbin matakai ne da Amurka ta dauka tun bayan da kasar ta yi wa wani bangare na takunkumin da ta sakawa kasar Cuba gyaran fuska a shekarar da ta wuce.

A watan Disamba na shekarar 2014 ne, kasar Amurka da kasar Cuba suka sanar da sake dawo da dangantakar diflomasiyyar dake tsakanin kasashen biyu, a watan Yuli na shekarar 2015 kuma, kasashen biyu suka farfado da dangantakar diflomasiyyar a tsakaninsu a hukunce, sai dai har ya zuwa yanzu, kasar Amurka ba ta kawar da dukkan takunkumin da ta kakabawa wa kasar Cuba na sama da rabin karni ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China