Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry kan harkokin manyan tsare-tsaren kasar Marie Harf ta bayyana cewa, kafa tutar kasar Cuba a majalisar gudanarwar kasar Amurka ya kafa sabon tarihi.
A bisa yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, yau ta kasance tarihi kan yadda kasashen biyu suka sake bude ofisoshin jakadancinsu a kasashen, kuma ofisoshin da suka wakilci kasashen biyu za su kasance ofisoshin jakadancinsu a na gaba. (Maryam)