Raul Castro ya ce, kasashen biyu sun amincewa, akwai sabani a tsakaninsu, amma duk da haka babu wani batun da ba za a iya tattaunawa a kan tebur ba, kasarsa na shirya sosai domin yin tattaunawa da kasar Amurka kan wasu batutuwan da suka haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren kuma, Barack Obama ya ce, ganawar tasu na da muhimmiyar ma'ana a cikin tarihin kasashen biyu, kuma a halin yanzu, ya kamata a dauki wasu sabbin matakai domin ciyar da yunkurin daidaita dangantakar kasashen biyu gaba. (Maryam)