Jiya Jumma'a 29 ga wata, majalisar gudanarwa ta Amurka ta sanar da cewa, ministan harkokin wajen kasar John Kerry ya tsai da kudurin fitar da kasar Cuba daga jerin kasashen dake goyon bayan ta'addanci tun daga wannan rana, wannan matakin da kasar Amurka ta dauka zai ba da babban taimako ga farfado da dangantakar diflomasiyya dake tsakanin Amurka da Cuba.
Kana, cikin wata sanarwa da majalisar gudanarwar kasar Amurka ta fidda, an ce, John Kerry ya tsai da wannan kuduri domin kwanaki 45 sun riga suka wuce, bayan majalisar gudanarwar kasar ta gabatar da rahoton fitar da kasar Cuba daga jerin kasashe masu goyon bayan ta'addanci ga majalisar dokokin kasar Amurka. (Maryam)