Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da sabon kakakin majalisar dokokin kasar Masar Ali Abadelaal a ci gaba da rangadin da ya ke a yankin gabas ta tsakiya.
Shugaba Xi ya bayyana tabbacin cewa, al'ummar Masar za su ci gaba da bayar da gudummawa a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya.
Ya ce, kasar Sin a shirye take ta karfafa ziyarce-ziyarce tsakanin manyan jami'an kasashen biyu tare da fadada musaya da hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da majalisun dokokin da jam'iyun siyasa da sauran kungiyoyin fararen hula na kasashen biyu.
Bugu da kari, kasar Sin ta bayyana kudurinta na kara zurfafa hadin gwiwa da mu'amala kan harkokin kasa da kasa tsakaninta da kasar ta Masar.
Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi shirin nan na "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta bullo da shi ya dace da manufofin raya kasa na kasar Masar.
Don haka ya yi kira ga kasashen biyu da su kara bunkasa matakan hadin gwiwa a fannonin da suka shafi ababan more rayuwa, sufuri, makamashi, harkar ilimi, yawon shakatawa da kuma tsaro, a wani mataki na kara bunkasa hadin gwiwar bangarorin biyu.
A nasa jawabin kakakin majalisar dokokin kasar ta Masar Ali Abdelaal ya yaba da irin kyakkyawar mu'amalar da ke tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu. Yana mai cewa, majalisar dokokin kasar Masar a shirye take ta zurfafa musaya da hadin gwiwa da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.(Ibrahim)