Mr. Xi Jinping ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin zantawar sa da sakataren kungiyar kasashen Larabawa ta AL Nabil Al-Arabi a kasar Masar, a ci gaba da ziyarar farko da yake gudanarwa a kasashen waje cikin wannan shekara.
Ya ce a matsayin kungiya mai matukar muhimmanci, AL na daukar matakan da suka kamata, wajen tabbatar da 'yancin al'ummun kasashen Larabawa, tana kuma taka rawar gani a batutuwan da suka jibanci shiyya-shiyya da ma na duniya baki daya.
Daga nan sai shugaban na Sin ya yi fatan cewa kungiyar za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen fadada zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kuma sauran kasashen Larabawa. Bugu da kari shugaba Xi ya jaddada aniyar kasarsa, game da ci gaba da marawa kungiyar AL baya, a yunkurinta na magance matsalolin dake addabar kasashen Larabawa ba tare da tsoma baki daga wasu sassan na daban ba. (Saminu)